1 John 3

1Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ʼyaʼyan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba ta san mu ba shi ne don ba ta san shi ba ne. 2Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ʼyaʼyan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa saʼad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake. 3Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda yake da tsabta.

4Duk mai yin zunubi yana karya doka ne; tabbatacce, zunubi karya doka ne. 5Sai dai kun san cewa ya bayyana ne domin yǎ ɗauke zunubanmu. A cikinsa kuwa babu zunubi. 6Ba mai rayuwa a cikinsa da yake cin gaba da yin zunubi. Ba wanda yake cin gaba da yin zunubi da ya taɓa ganinsa, ko ma ya san shi.

7ʼYaʼyana ƙaunatattu, kada ku yarda wani yǎ sa ku kauce. Duk mai yin abin da yake daidai mai adalci ne, yadda yake mai adalci. 8Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun daga farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yǎ rushe aikin Iblis. 9Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah. 10Ta haka muka san waɗanda suke ʼyaʼyan Allah da kuma waɗanda suke ʼyaʼyan Iblis: Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗanʼuwansa.

Ku Ƙaunaci Juna

11Wannan shi ne saƙon da kuka ji tun daga farko: Ya kamata mu ƙaunaci juna. 12Kada ku zama kamar Kayinu, wanda ya zama na mugun nan, ya kuma kashe ɗanʼuwansa. Me ya sa ya kashe shi? Domin ayyukansa mugaye ne, na ɗanʼuwansa kuma na adalci ne. 13Kada ku yi mamaki ʼyanʼuwana, in duniya ta ƙi ku. 14Mun san cewa mun riga mun ratsa daga mutuwa zuwa rai, domin muna ƙaunar ʼyanʼuwanmu. Duk wanda ba ya ƙauna matacce ne har yanzu. 15Duk mai ƙin ɗanʼuwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa.

16Ga yadda muka san mece ce ƙauna: Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ʼyanʼuwanmu. 17In wani yana da dukiya ya kuma ga ɗanʼuwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, yaya ƙaunar Allah za ta kasance a cikinsa? 18ʼYaʼyana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai da aikatawa da kuma gaskiya. 19Ta haka muka san cewa mu na gaskiya ne, har muna kwanciyar rai a gabansa 20a duk saʼad da zukatanmu suka ba mu laifi. Gama Allah ya fi zukatanmu, ya kuma san kome.

21Abokaina ƙaunatattu, in zukatanmu ba su ba mu laifi ba, muna da ƙarfin halin tsayawa a gaban Allah ke nan 22muna kuma samun dukan abin da muka roƙa daga gare shi, domin muna biyayya da umarnansa muna kuma yin abin da ya gamshe shi. 23Umarninsa kuwa shi ne: mu gaskata da sunan Ɗansa, Yesu Kiristi, mu kuma ƙaunaci juna kamar yadda ya umarce mu. 24Waɗanda suke biyayya da umarnansa kuwa suna rayuwa a cikinsa, shi kuma a cikinsu. Ta haka kuwa muka san cewa yana raye a cikinmu: Mun san haka ta wurin Ruhun da ya ba mu.

Copyright information for HauSRK